Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na samar da karin wasu kotunan shari’ar Muslunci guda 3, bayan da kotun ta sauya wasu kotunan matsugunan daga ainihin inda suke a baya.
Batun sauya musu Matsugunin ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin cewa hakan wata dama ce ga gwamnatin na cefanar da ainihin wuraren da kotunan suke tun Fil’azal.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na manyan kotunan Shari’ar addinin Musulunci Muzammil Ado Fagge ya fitar a ranar Lahadin karshen mako, ya ce yanzu haka ana aikin samar da wasu ƙarin kotunan.
KARANTA ANAN: Kaduna: El-Rufai Ya Yi Allah-wadai Da Hallaka Wasu Makiyaya Da ’Yan Daba Suka Yi A Jihar
Ya ce an samu ƙarin sabbin kotunan Shari’ar addinin Musulunci guda 3 da aka gina su a unguwar Ɗanbare Byepass dake ƙaramar hukumar Kumbotso.
Muzammil Ado Fagge ya ƙara da cewa wannan babban ci gaba ne wanda aka same shi bisa jagorancin Girandi Khadi na jihar Kano, da magatakardar kotunan Shari’ar addinin Musulunci na jahar Kano.
A kwanakin baya ne dai ake zargin gwamnatin jihar Kano da cefanar da wasu daga kotun Shari’ar Addinin Musulunci.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ta bakin kwamishinan Shari’a Musa Abdullahi Lawan da cewa ba siyar da su aka yi ba, illa sauya musu waje da gwamnatin ke kokarin yi, sakamakon sun shiga cikin kasuwa kuma ita kotu tana buƙatar waje mai nutsuwa.
A wani labarin kuma: ‘Yan Najeriya Miliyan 15 Ne Ke Amfana Da Ayyukan Samar Da Ruwan Sha – FG
Akalla ‘yan Najeriya miliyan 15 ne ke cin gajiyar ayyukan samar da ruwan sha a sassa daban-daban na kasar nan.
Ministan albarkatun ruwa, Malam Suleiman Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin nan yayin da yake amsa tambayoyi, a matsayin bako a dandalin kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Abuja.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Adamu ya ce gwamnati mai ci ta gaji ayyukan da ba a kammala ba a lokacin da ta hau mulki a shekarar 2015.