Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ziyarci wurin da aka samu fashewar tukunyar gas a yankin Sabon Gari dake birnin Kano.
Osinbajo wanda yake ziyarar neman kuri’un wakilan jam’iyyar APC a jihar Kano, ya nuna alhini kan abun da ya faru, tare da jajantawa iyalan wad’anda iftila’in ya rutsa da su.
Kazalika, Osinbajo ya jaddada kudirin aniyar gwamnatin tarayya na kare rayuka da kuma dukiyoyin al’ummar kasarnan.
Gwamnan Kano wanda suke tare da mataimakin shugaban Kasar, ya ce sun je wajen ne domin jajantawa wadanda iftila’in fashewar Gas ɗin ta rutsa da su.
Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ce zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin wani abu makamancin hakan bai sake faruwa ba, ta hanyar daukar matakan da suka kamata.
Yanzu dai haka an ceto wasu da dama wa’danda ginin ya danne, duk da cewa Hukumomi basu bayyana adadin waɗanda suka mutu, da kuma jikkata ba.