Firaministan Spaniya Pedro Sanchez ya bayyana aniyar gwamnatin kasar ta yi wa yan awaren yankin Kataloniya afuwa.
A shekara ta 2017 ne dai aka daure shugabannin yankin tara bayan da Kudirin su na kafa sabuwar kada ya gaza samuwa, kazalika an kama wasu uku da laifin bijire wa gwamnati to sai dai su sun tsallake rijiya da baya.
A gobe talata ne ake sa ran mika takardar afuwar tasu gaban majalisar dokokin kasar ta Spaniya.
Dubun-dubatan jama’a ne a farkon watan nan suka yi zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin na yin afuwar, to sai dai gwamnatin ta ce hakan zai yayyafa ruwa wa wutar rikicin ɓallewar kasar.
Kimanin shekara huɗu kenan yan Kataloniyar ke fafutukar ɓallewa daga Spaniya, lamarin da ya kai ga ya sanya kasar cikin rikicin siyasar da ba ta taɓa fadawa ciki ba a tsawon shekara 40.
Sai dai yan adawa sun soki matakin gwamnati inda suke ganin tana amfani da hakan ne wajen cimma muradun ta.