Gwamnatin jihar Katsina ta saki ‘yan bindiga guda shida da jami’an tsaro suka kama a wani mataki na sulhuntawa da gwamnatin ta dauko da ‘yan bindigar domin samun dawwamammen zaman lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Masari ya ziyarci kananan hukumomin Dandume, Sabuwa, Faskari, Kankara, Safana, Danmusa, Batsari da kuma Jibiya a jihar sakamakon yadda ‘yan bindigan suka zafafa kai hare-hare kananan hukumomin. Wannan lamarin ya sanya gwamna Masari yin sulhu da shugabannin ‘yan bindigar a makon da ya gabata, inda aka cimma yarjejeniyar cewa za a saki wadansu daga cikin ‘yan bindigar da jami’an tsaro suka kama.