Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware ma jihar Katsina guraben kujerun aikin hajjin 2023 guda 4,913. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu-Kuki, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Katsina lokacin da yake zantawa da manema labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
Ya ce za a bukaci maniyyatan da ke da niyyar ajiye mafi karancin Naira miliyan 2.5 a wurin hukumar har zuwa lokacin da NAHCON za ta sanar da fara biyan kudin da za ta biya.
“A bisa karbar kujerun aikin hajji 95,000 da Masarautar Saudiyya ta amince wa Najeriya, hukumar alhazai ta kasa ta ware guraben kujeru aikin Hajji 4,913 ga jihar Katsina.
“Gwamna Aminu Masari bisa ga wannan adadi, ya amince da sake raba wa kananan hukumomi 34 domin gudanar da aikin hajji da kuma saukaka ci gaba da yi wa maniyyata rijista a fadin jihar nan.
Nuhu-Kuki ya kuma shaida wa manema labarai cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara shirye-shiryen karantar da alhazai da fadakarwa a shiyyoyin ta daban-daban. (NAN)
A wani labari kuma, Jiga-Jigan Jam’iyar APC A Adamawa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
Mambobin kungiyar Nuhu Ribadu Support Group da Tinubu Foundation a jihar Adamawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Wannan dai na zuwa ne saura kwanaki biyar a gudanar da babban zaben kasa.