A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Katsina ta sanar da dakatar da kungiyar sa kai da ake kira Yan sa Kai a jihar nan take.
“ayyukan aikata laifuka” na mambobinta kafin yanke shawarar.
Kungiyar dai ta kunshi masu aikin sa kai ne da ke ikirarin taimakawa al’amuran dake fama da rashin tsaro.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, ya fitar, ta yi zargin cewa wasu ‘yan kungiyar na aikata kisa ba tare da bin ka’idojin shari’a ba.
Sanarwar ta kara da cewa kungiyoyin ’yan banga ne kawai wadanda mambobinsu ke aiki a karkashin rundunar ‘yan sanda ne kadai, gwamnatin jihar za ta amince da su.
Sanarwar mai taken, ‘Hana ayyukan kungiyar sa kai a fadin jihar Katsina’.
A cewarta, “Gwamnatin jihar Katsina ta haramta ayyukan ‘Yan Sa Kai, sakamakon yadda korafe kofe kan kungiyar ‘yan sa kai (Yan Sa Kai) ta yi wa jihar katutu, wanda a kodayaushe ke haifar da kashe-kashen mutane da ba su ji ba ba su gani ba, tare da wawure dukiyoyinsu.
“Gwamnatin jihar Katsina ta amince da ayyukan kungiyar ‘yan banga ne kawai da ke karkashin kulawa da kuma sanya ido na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da cibiyoyin gargajiya.
“Daga yanzu, a mika wadanda ake tuhuma ga ‘yan sanda ko kuma hukumar tsaro domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace. Kada kowa ya ɗauki doka a hannunsa, a ƙarƙashin kowace irin yanayi.