Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa ta shirya yi wa mutum miliyan bakwai allurar rigakafin cutar shawara ko kuma ‘Yellow Fever’ a turance, da take ci gaba da yi a fadin jihar.
Wannan rigakafin ya biyo bayan samun mutum 36 da aka yi da cutar a kananan hukumomin Danmusa da Kankara a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Mannir Yakubu, shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake kaddamar da shirin a ranar Litinin a Katsina, inda ya nemi dukkanin al’umma da su tabbata sun amfana da wannan shirin.