• Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Abubakar Babudu ta amince da Gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda 36.
• Kwamishinan Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, Jafar Muhammad ne ya bayyana wannan ci gaban.
• Ya ce tuni akagra wasu sama da 100 a jihar Kuma anyi hakan ne domin farfado da fannin kiwon lafiya a fadin jihar.
Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya kaddamar da yaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 36, domin inganta fannin kiyon lafiya a fadin jihar baki daya.
Kwamishinan fannin kiwon lafiya na jihar, Jafar Muhammad ne ya bayyana cewa, za a yi gyare-gyaren cibiyoyin kiwon lafiyan ne, a wani Shari na tseratar da rayuwar al’uma sama da milliyan daya a fadin jihar, Kuma don samun dai-daito a fannin kiwon lafiya.
” Tuni aka kammala gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda dari da talatin da hudu a jihar, domin inganta fannin a matakin farko” inji Kwamishinan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ruwan sama ya kashe Mutum biyu, ya lalata gine-gine sama da 1,500
” Gyaran guda 36, zai taimaka wajan farfado da fannin kiwon lafiya a matakin farko” inji shi.
A wani labarin kuma na daban
Hukumar bada agajin gaggawa SEMA reshen jihar Katsina ta ce, gine-gine sama da dubu 15,000, saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar ya lalata, a ranar Litinin din da ta gaba.
Mai Magana da yawun hukumar Umar Mohammed ya bayyana cewa, Akalla kananan hukumomin uku ne lamarin ya shafa.
Muhammed ya kara da cewa, a yau Laraba cikin gine-gine 1500, gidaje 800 lamarin ya shafa. Inda ya hadar da kananan hukumomin Faskari, Bindawa da kuma karamar hukumar Sabuwa.
Kazalika ya ce, a karamar hukumar Bindawa, inda akasami ruwan saman da ya kwashe akalla awa biyar, ya yi sanadiyar mutuwar Mutum biyu.
Rahotanni sun nuna cewa, ruwan saman ya fara ne da musalin karfe 10 na safen ranar Litinin, Inda ya kai har musalin karfe hudu na yammaci, Wanda ya tilastawa masu motoci aje ababen hawan su.
Wasu mazauna yankin da lamarin ya shafa sun tattauna da Kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN cewa, su na cikin damu wa matuka, sanadiyar toshewar hanyoyi da ruwan saman ya janyo.
Daya daga cikin matuka Mota da ke yankin Mai suna Muhammad Safana ya ce, lamarin zai iya kazanta, Indai dai ruwan saman ya cigaba da sauka.
Comments 1