By Abbas Yakubu Yaura
Akalla shanu 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Alhamis a Lokoja dake jihar Kogi.
Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa mutuwar shanu data afku ana zargin guba ce ta hadda sa faruwar lamarin.
DUBA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar APC Ta Ayyana Fom Din Tsayawa Takara Ga Mata Kyauta Ne
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin jihar Kogi ta gargadi al’ummar jihar musamman na yankin Lokoja da su daina cin naman sa nan da mako guda.
Daraktan kula da dabbobi na jihar, Dakta Salau Mohammed Tarawa, ya yi wannan gargadin a ranar Alhamis.
Ya ce da samun rahoton, jami’an ma’aikatar sun dauki matakin nemo wasu matattun shanun da ke kasuwa ana sayarwa.
Ya ce an kai wasu shanun garuruwan Osara, Ajaokuta, Obajana, Koton Karfe da Kakanda domin a sayar da su ga jama’a da ba su ji ba gani.
Tarawa ya ce tuni ma’aikatar noma ta hada kai da jami’an tsaro domin gayyato makiyayan da lamarin ya shafa domin yi musu tambayoyi tare da tabbatar da daukar matakin da ya dace a kansu.
Babban sakataren dindindin, Malam Sani Abdulganiyu, ya bukaci jama’a da su baiwa ma’aikatar hadin gwiwa domin shawo kan lamarin ba tare da illa ga lafiyarsu ba.