Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi shugabannin makarantun jihar da su daina karbar kudaden haram a duk makarantun sakandaren gwamnati.
Babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi da ci gaban bil’adama ta jihar, Mrs Mary Kemi Adeosun, ta bayyana haka a wata ganawa da dukkan shugabannin makarantun sakandire na jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cin Hanci Da Rashawa Ya Kawo Cikas Ga Cigaban Afirka – Shugaba Buhari
Ta ce duk shugaban makarantar da aka kama yana karban kudaden harajin na kungiyar iyaye da malamai (PTA) da gwamnati ta amince da shi za a hukunta shi kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada.
Babbar Sakatariyar ta ce, “Ma’aikatar za ta tura jami’an binciken kudi zuwa dukkan makarantun Sakandare da ke jihar domin sanin halin da ake ciki a asusunsu.”
Adeosun, wacce ta nemi goyon bayan shugabannin makarantun ga gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ta kara da cewa gwamnati ta dukufa wajen ganin an kyautata rayuwar malaman da ke da jari mai yawa a fannin ilimi.
Ta yi kira da a tabbatar da hankali da da’a a fadin makarantun sannan ta bukaci shugabannin makarantun da su rika hakuri da juna domin a samu zaman lafiya a makarantunsu.
Kazalika ta bukaci shugabannin makarantun su rika sanya dalibansu a gida, tana mai cewa duk makarantar da aka samu daliban suna yawo a kan titi suna iya fuskantar takunkumin gwamnati.
Tun da farko, shugaban zartarwa na Hukumar Koyarwa ta Jihar Kwara (TESCOM), Malam Bello Taoheed Abubakar, ya bayyana a matsayin jita-jita na karya, labarin da hukumar ta yi na sayar da nadin shugabanni da mataimakan shugabannin makarantun sakandare na jihar.
A wani labarin kuma, UNGA77: Najeriya Ta Nuna Iya Aiki Wajen Dawo Da Kadarorin Da Aka Wawure – Malami
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce Najeriya ta nuna yadda za a yi amfani da kadarorin da aka kwato domin samun ci gaba mai dorewa.
Malami ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa a wani babban taron da aka yi a kan “Muradin Tsaron Abinci: Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma tabbatar da dawo da kadarorin da aka wawure don ci gaba mai dorewa”, a gefen babban taro na 77 na Majalisar Dinkin Duniya.