Gwamnatin Jahar Lagos ta hana amfani da dukkanin nau’ikan Lasifiku a tashoshin Motoci a faɗin Jahar.
Mai Baiwa Gwamna Shawara na musamman akan Sufuri Oluwatoyin Fayinka, ya sanar da hakan a lokacin taron Hukumar Kula da Mahalli ta Ƙasa.
Daga yanzu, duk wanda aka kama yana haɗa wata Lasifika, zai fuskanci hukuncin doka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dole ne a hukunta masu shigo da gurbataccen man fetur – Buhari
Yace Kwamitin Tashar Motoci an bashi umarni ya bi dukkanin tashar Motoci domin tabbatar da an bi dokar.
Babban Sakataren Ma’aikatar Mahalli da Albarkatun Ruwa Tajudeen Gaji ya bayyana rashin jindaɗi akan haddasa surutai.