Gwamnatin Jahar Lagos tasha alwashin biyan kuɗin maganin waɗanda aka ceto a ginin daya rufta a yankin Ikoyi na Jahar a ranar Litinin.
Haka zalika Gwamnatin Jahar ta jaddada ƙudirin ta na ganin an ceto mutane da dama a raye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Gwamnan Anambra: Obaseki ya buƙaci a zaɓi Ɗan takarar Jam’iyyar PDP
Wannan na ƙunshene a cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jahar ta fitar a ranar Talata, inda sanarwar tace Mataimakin Gwamnan Jahar Obafemi Hamzat ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru da ƴan uwan waɗanda lamarin ya rutsa dasu, a lokacin da ya duba aikin ceto mutanen dake cikin ginin da Hukumomin Gwamnati ke gudanar wa.
“Mataimakin Gwamnan wanda ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati, yace abinda gwamnatin ta sanya a gaba, shine ta tabbatar dacewa aikin ceto mutanem ya haifar da Ɗa mai ido, gami da samun nasarar ceto wanda suke ciki a halin yanzu a raye,” inji sanarwar.
An naƙalto Hamzat na cewa, “mutane 9 aka ceto a raye, tare da kaisu Asibiti, a yayinda aka samo gawar mutane 10 da suka mutu. Daga cikin waɗanda suka rayu guda 9, uku daga ciki an sallame su daga Asibiti, guda 6 kuma suna samun sauƙi.
Acewar sanarwar “Hamzat yace da wahala a iya tantance ainahin mutane nawa ne lamarin ya rutsa dasu, yana mai bayyana cewa ginin har yanzu shi ake yi, kuma babu wanda suke zaune a ciki.
Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Jahar a ƙoƙarin ta na tabbatar da cewa duk wani gini da ake ginawa sai an tabbatar da ingancin shi, domin magance sake afkuwar lamarin.
Comments 1