Gabanin ranar 1 ga watan Yuni, 2022, wato dai ranar da dokar haramta masu tuka baburan Achaba ‘yan kasuwa, wadanda aka fi sani da masu “Okada”, aiki a wasu yankunan jihar.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar Legas ta kammala shirin kaddamar da kungiyar Anti-Okada domin aiwatar da aikin hana Achabar.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda tun farko ya bayyana shirin hana ayyukan Okada a kananan hukumomi 6 wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Yuni, 2022, makonni biyu da suka gabata, ya dage kan aiwatar da dokar.
Ranar da aka sanya bayan roko daga shugabannin kungiyar Okada, wadanda suka bukaci a tsawaita domin fara aiwatar da dokar.
Kwamishinan Sufuri, Dr. Fredrick Oladeinde, a yau Talata, ya ce manufar kafa tawagar ita ce tabbatar da aiwatar da doka da Oda.
A cewar Oladeinde, “A daidai lokacin da aka fara hana zirga-zirgar babura a cikin ƙananan hukumomi (6) ma’aikatar sufuri tana kaddamar da rundunar yaki da Okada.
”Wannan taron yana gudana ne da karfe 2:00 na rana a dakin taro na Adeyemi Bero, Sakatariya, Alausa, Ikeja.”
Ku tuna cewa Sanwo-Olu a ranar 10 ga Mayu, 2021, ya sake duba dokar zirga-zirgar Legas ta 2012 da ke jagorantar ayyukan Okada, bayan da gwamnatocin da suka gabace shi, Babatunde Fashola da gwamnatin Akinwunmi Ambode suka haramta ayyukansu.
Fashola ya rattaba hannu kan dokar zirga-zirgar ababen hawa ta Legas 2012, wadda ta takaita ayyukan okada a akalla 492 daga cikin 9200 da ke cikin babban birnin kasar, a kokarinsu na rage barazanar ayyukansu a baya-bayan nan.
Comments 1