Gwamnatin jihar Legas ta umarci dukkan makarantu da su fara zagon karatun shekarar 2022/2023 a ranar 5 ga watan Satumbar 2022.
Bayanan hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan ofishin tabbatar da ingancin ilimi na jihar, Abiola Seriki-Ayeni, ya fitar a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sha’aban Sharada Ya Ƙaddamar Da Takararsa A ADP Bayan Shan Kaye A APC
An yi nuni da cewa hakan ya kasance kamar yadda kwamishiniyar ilimi ta jihar, Misis Folasade Adefisayo ta amince.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Dukkanin makarantun da ke a matakin farko da manyan makarantu a jihar Legas an umurce su da su koma zangon farko a ranar Litinin 5 ga watan Satumba, 2022 kamar yadda aka bayyana a cikin Kalandar ta zangon karatu na shekarar 2022/2023,bisa amincewar kwamishiniyar ilimi Misis Folasade Adefisayo.
“Kalandar ilimi ta ba da fifiko ga daidaitattun ranakun karatu kuma makarantu shine tabbatar da bin doka da oda don samar da ingantaccen ilimi mai dorewa a jihar Legas.”
“Dalibai da ma’aikatan da ke makaranta ana maraba da su zuwa makarantu kuma ana sa ran za su bi ka’idojin lafiya da aminci na makaranta.”
Sanarwar ta kara da cewa ana iya saukar da manhajar kalandar karatun daga gidan yanar gizon tabbatar da ingancin ilimi na jihar Legas.
A wani labarin kuma, Yajin Aikin ASUU: FG Ta Jaddada Ci Gaba Da Tafiya Kan Tsarin Babu Aiki Babu Biya
Karamin Ministan Ilimi, Rt Hon Goodluck Nanah Opiah, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin tarayya ta tsaya kan tsarin babu aiki, babu biyan albashi ga malaman jami’o’i ASUU.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kungiyar malaman jami’o’in, ASUU, tuni tayi Allah wadai da wannan tsarin na gwamnatin tarayyar.