Gwamnatin Jihar Legas ta bai wa kowanne dan Nijeriya da aka dauko daga Afrika ta Kudu a ranar Laraba, tallafin Naira dubu 20.
A wannan karo tawaga ta biyi, ‘yan Nijeriyar 319 ne aka sauke a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
An dawo da su ne mako daya bayan fara kwaso wasu 178 da aka fara daukowa, bayan kashe-kashen kin jinin baki da ‘yan Afrika ta Kudu suka zafafa.
Jirgin kamfanin Air Peace ne ke jigilar dawo da su gida Najeriya kyauta.
Air Peace kirar B777 ne ya dauko tawagar da ta sauka ranar Laraba, su 319 a Legas. Bayan saukar ta su ce kuma gwamnatin jihar Legas ta bai wa kowanen su naira 20,000.
Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Nijeriya dake Kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce tare da Allen Onyema, mai kamfanin Air Peace, tare da Mai Taimaka Wa Gwamnan Legas kan Ayyuka na Musamman, Jermaine Sanwo-Olu suka yi musu kyakkyawar tarba a filin jirgin na Legas.