By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Legas tace an gina bandakuna 345 na jama’a a fadin jihar a wani yunkuri na magance matsalar bahaya a fili.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Mista Tunji Bello, ne ya bayyana hakan a yayin bikin ranar bandaki ta duniya na shekarar 2021 da aka gudanar a ranar Juma’a.
Bello ya samu wakilcin mai ba da shawara na musamman kan harkokin magudanar ruwa da Kuma samar da ruwan sha , Mista Joe Igbokwe a wajen taron.
Yace, “Jihar ta gina bandakunan jama’a guda 345 a wurare masu muhimmanci a fadin birnin, yayin da kuma masu gudanar da bandaki masu zaman kansu 615 ne aka yi musu rijista.
Waɗannan nasarorin sun kasance sakamakon dabarun juriya da aka ɓullo dasu a matsayin daftarin aiki don inganta rayuwar mazauna jihar Legas.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito “yana da mahimmanci a lura cewa a halin yanzu Najeriya ce ke kan gaba a matakin yin bahaya a fili kuma ana sa ran kowace Jiha a kasar nan za ta yi amfani da sanarwar gwamnatin tarayya na samar da matsayin daina yin bayan gida a fili nan da shekarar 2025.”
Har ila yau, Sakatariyar dindindin na Ofishin Kula da Muhalli, Misis Belinda Odeneye, wadda Daraktan Kula da Muhalli Mista Sheriff Savage ya wakilta, tace gwamnati ta fara wayar da kan al’umma kan tsaftar muhalli da kuma tsafta jiki.