By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar Legas da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, a ranar Laraba, sun kaddamar da wani jirgin ruwan marasa lafiya a matsayin wani shiri na fadada ayyukan daukar marasa lafiya zuwa yankunan da suke da kogi na jihar.
Babban Manajan LASWA, Mista Oluwadamilola Emmanuel, ya bayyana cewa kaddamar da Jirgin ruwan wani shiri ne na kara hada kan tsarin gaggawa da ceto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanatocin Jam’iyar APC 22 Na Daf Da Komawa Jam’iyar PDP—— Femi Fani-Kayode
Ya ce, “A hankali muna gina wannan aikin, kuma mun ga yadda tsaro a hanyoyin ruwa ke ci gaba da inganta kowace shekara.
“Abin da muke shirin yi a halin yanzu shine samun namu ainihin kayan gaggawa da jirgin ruwan mayar da martani tare da Jet Ski da dakin sarrafawa da za a kaddamar nan ba da jimawa ba.”
Babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, Mista Olusegun Ogboye, ya bayyana a wajen taron cewa, jirgin ruwan zai fi magance matsalolin gaggawa na kan ruwa da kuma samar da ayyukan wayar da kan al’umman dake kan kogi da gefensa.
Ya ce, “Ma’aikatar lafiya za ta kuma samar da kayan aikin dan adam da kayayyakin amfani don samar da lafiya. Jihar ta yi shirin samun karin jiragen ruwa domin tabbatar da cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata tare da biyan bukatun jama’ar jihar Legas.”
Comments 1