Rahotanni na nuni da cewa; Gwamnatin jihar Legas ta shirya fara ayyukan ceto “don duba kasuwanni, gine -ginen da ba a kammala ba da karkashin gadoji domin kakkabe mabarata da sauran gajiyayyu da ke zaune a wuraren da ba su dace ba.
To sai dai mabarata a wani taron manema labarai a karkashin Sarkin Makafin jihar Legas sun bayyana cewa wannan ceto na gwamnatin jihar Legas, a matsayin wani mataki na cin mutuncinsu da kuma jefa rayuwarsu da ta iyalansu cikin wani yanayi na tsaka mai wuya.