Gwamnatin Jihar Katsina a Karkashin Jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari,ta fara aikin yin magani ga masu lalurar tabin hankali su 500 a fadin Jihar.
Shirin wanda zai karade Kananan Hukumomi 34 dake Jihar tuni ya fara kula da masu lalurar su 178 a fadin Kananan Hukumomi 7 da shirin ya fara aiki.
Daga cikin mutanen su 178,a halin yanzu an kwantar da kimanin mutane 20 a Asibitin Kula Da Masu Tabin Hankali Na Katsina domin samun kulawa ta musamman.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ruftawar ginin Ikoyi: Gwamnonin Arewa Maso Yamma sun ziyarci wurin, sun jajantawa iyalan da lamarin ya shafa
Kamar yadda Kafar Yada Labarai ta The Fact 24 ta ruwaito Gwamnatin ta Alhaji Aminu Bello Masari,ta samar da kayan abinci da magunguna da sauran duk kayayyakinda ake bukata domin ganin shirin ya samu nasararda ake bukata.
Irin wannan shiri na kula da masu lalurar tabin hankali wanda ba shi bane karo na farko,ya haifar da sakamako mai kyau ta la’akari da yawan masu lalurar da suka dawo cikin hayyacinsu.
A halinda ake ciki wasu da aka kula da su a irin shirin da aka gudanar a shekararda ta gabata,wasunsu sunyi Aure kuma suna gudanar da harkokin rayuwarsu yadda ya kamata kamar kowa.
A dukkan Kananan Hukumomi da shirin ya fara ziyarta a halin yanzu,Kwamishinan Ma’aikatar Alhaji Sani Aliyu Danlami ya bukaci al’umma su bayar da cikakken goyon bayanda ya dace ga shirin.
Kafar Yada Labarai ta The Fact 24 ta tsinkayi Kwamishina Danlami tana yabawa Gwamna Masari akan samar da dukkannin abubuwanda ake bukata don ganin an cimma kyakkyawan sakamako.