Gwamnatin Najeriya na Neman Tallafin Biliyan 681 Don Ƙidayar Al’umma a 2023
Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce ana bukatar karin N681bn domin samar da ingantacciyar kidayar jama’a a shekarar 2023.
A wani taro da aka yi da masu hannu da shuni a Abuja ranar Alhamis, an fitar da N111bn daga cikin N178bn da aka ware wa hukumar kidaya ta kasa a shekarar 2022 domin shirye-shiryen kidayar jama’a a badi.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP ta caccaki Buhari kan yajin aikin ASUU, ta ce Gwamnatin APC ta ɗauki nauyin ta’addanci
Ya ce kasar ba za ta iya samar da kudaden kidayar jama’a ita kadai ba don haka akwai bukatar neman taimako daga abokan huldar kasashen waje da na cikin gida.
Osinbajo ya ce gwamnati ta nuna himma wajen aikin kidayar jama’a ta hanyar kashe karin N21bn wajen yin taswirori.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce saboda kalubalen da ke kawo cikas ga kidayar jama’a a baya, gwamnati ta tallafa wa NPC don gudanar da kidayar jama’a da kawo sauyi ta hanyar tura fasahar zamani a shekarar 2023.
Ya ce an dukufa wajen samun kayan aiki da za su samar da kidayar jama’a cikin nasara.
Shugaban NPC, Nasir Isa Kwarra, ya ce don tabbatar da yin lissafin kudaden da aka bayar, wadanda aka bayar a Naira za su zauna da babban bankin Najeriya; yayin da kudaden kasashen waje za su kasance tare da asusun Majalisar Dinkin Duniya.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Anambra ta rufe otal saboda bikin Jima’i
Gwamnatin jihar Anambra ta dakatar da ayyuka a wani sashe na Otel ɗin Wintess Garden Annex da ke Awka, babban birnin jihar, inda ake zargin an gudanar da shagalin jima’i a karshen makon da ya gabata.
Bidiyon da ya yi ta yawo a yanar gizo na wani biki da aka gudanar a Otel na Wintess Garden Annex, Ifite Awka, an ga mahalarta Taron suna jima’i a tsakaninsu.