Gwamnatin Tarayya ta sake jaddadawa ‘yan kasar cewa tana dab da ɗage haramcin daina amfani da shafin Twitter a faɗin ƙasar nan bada jimawa ba.
Ministan yaɗa labarai da raya al’adu, Lai Mohammed ya tabbatar da hakan ne a lokacin amsa tambayoyin ‘yan jarida a fadar gwamnati, bayan taron majalisar zartarwa a Abuja.
Sai dai ministan bai sanar da hakikanin ranar ɗage haramcin ba, ko ranar da za a koma amfani da shafin, amma tattaunawa tsakaninsu da masu shafin na tafiya babu cikas cikin mutuntawa, a cewarsa.
A jiya Talata aka cika kwana 100 da haramcin daina amfani da Tuwita, bayan da gwamnati ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yaɗa labaran karya da ke iya haddasa ”tashe-tashen hankula”.