By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta amfani da kuma sayar da gawayi a jihar domin kare muhalli.
Mista Aliyu Agwai, Babban Sakatare na Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Kasa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Lafiya.
Yace hanyar samar da gawayi na da illa ga muhalli ta hanyar lalata yanayi da karuwar dumamar yanayi.
Agwai ya lura cewa kona gawayi, musamman na haifar da hayaki mai lahani.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Yanke bishiyu na iya haifar da asarar wurin zama ga nau’in dabbobi, wanda zai iya cutar da yanayin halittun dake rayuwa a cikin dajin.
“Kusan dukan dabbobi da shuke-shuke na ƙasa suna rayuwa a cikin dazuzzuka kuma da yawa ba za su iya tsira daga sare dazuzzuka da ke lalata gidajensu ba,” in ji shi.
Ya kuma gargadi masu sayar da gawayi dasu guji gurfanar da su a gaban kuliya idan suka saba dokar.
A halin da ake ciki wata kotun tafi da gidanka da ke kula da shari’o’in da suka shafi muhalli, ta gurfanar da wasu mutane 32 da ake zargi da karya dokar tsaftace muhalli a birnin Lafiya.
Dan sanda mai shigar da kara, Mista Abubakar Mohammed, wanda kuma babban jami’in kula da muhalli ne, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin suna yin mu’amala da sana’o’insu na kashin kansu a yayin da ake ci gaba da aikin tsaftar muhalli.
Mohammed yace laifukan sun sabawa sashe na 9(2) na dokar kula da muhalli ta jihar.sannan ya bukaci kotun da ta sanya musu takunkumi don ya zama darasi ga wasu.
Alkalin kotun, Mista Abdullahi Lande, ya yanke musu hukuncin daurin watanni shida a gidan yari tare da zabin tarar Naira 5,000 zuwa naira 50,000 kowannen su.