Shugaban hukumar tsara burane na jihar Nasarawa Engr Mohammed Wada ya bayyana cewa, hukumar za ta rushe gine-gine guda 200.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake zanta wa da mane ma labarai a garin Lafiya babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne, biyo bayan gaza war masu wurin na rushe gine-ginen, bayan da hukumar ta aike musu da takaddar gargani har sau uku, amma su kayi burus da gargadin.
Ya ce, ” wasu daga cikin gine-gine sun toshe magudanar ruwa, ya yin da wasu kuma aka gina su, batare da ragista da hukumar da abun ya shafa ba” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Kallon Fim, ku dunga mana uziri, inji Khadeejah Mustapha
Shugaban ya kara da cewa, tuni hukumar ta hada guiwa da wasu hukumomi, domin tabbatar da bin doka, wajan tsare-tsare da kuma ci gaban jihar.
Kazalika ya kuma yi kira ga mazauna yankin, da su yi abun da ya dace.
A karshe ya kuma ce, hukumar kula da tsara burane ta jihar Nasarawa, yanzu tana harkokin ta a yanar gizo, inda kowa zai iya ziyartar adireshi hukumar domin yin ragista, ko kuma sabunta ragistan ginin shi, a ko Ina ya ke a fadin duniya.