By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Nasarawa ta baiwa matasa ‘yan kasuwa a jihar tabbacin samar musu da muhallin da zasu binciko abubuwan da zasu taimaka wajen ci gaban jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a a garin Lafiya yayin bikin rufe shirin horar da matasa 100 da aka zabo a tsakanin kananan hukumomin jihar 13 na shekarar 2021.
A yayin bikin, an shirya bikin baje kolin ayyukan yi ga matasa 100 tare da Gwamna Sule inda ya yi fatan hakan zai kara wa daliban da suka yaye kwarin gwiwar samun aikin yi da kuma gudanar da ayyuka masu ma’ana.
Gwamnan wanda mataimakinsa Emmanuel Akabe ya wakilta, ya bayyana cewa jajircewar gwamnatin sa na ganin an dawo da dukiyoyin matasa a jihar shi ya sa Oxfarm Nigeria ta nuna sha’awarta na bayar da misali da wata makarantar Bits Academy dake jihar Nasarawa za ta yi shekara guda tana koyar da yar da Shirin a ICT ga matasa marasa fasaha.
Sannan yace, “Baje kolin ayyukan yi da muke yi a yau ya zama wajibi domin zai taimaka matuka gaya wajen amfanar dasu da samun damar kawar da zaman banza da tsunduma su cikin harkokin da zasu inganta tattalin arzikinsu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnan ya yaba wa ofishin ci gaban bil Adama na jihar, Oxfam Nigeria da Poise Graduate Academy bisa nasarar shirin horar da matasa 100 na tsawon mako uku kan aikin yi da dabarun kasuwanci.