Gwamnatin jihar Neja ta sake fasalin kwamitin karta na kwana mai kula da ayyukan babura masu kafa biyu, wanda zai fara aikin daga karshen watan daya gabata, da nufin tsaftace harkar sufurin a jihar baki daya.
Babban sakataren ma’aikatar sufuri ta jihar Alh. Yunusa Nahauni, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yayin wani taro da suka gudanar da jami’an hukumar kula da sufuri ta VIO.
KARANTA ANAN: Osinbajo Ya Gabatar Da Wata Yarjejeniyar Musayar Bashi Da Sauyin Yanayi A Amurka
Nahauni ya kara da cewa sakamakon wannan gyare gyaren da aka yi yanzu kula da kwamitin kart a kwanan zai koma karkashin hukumar VIO da Traffic Vanguard wadanda suke aiki a jihar ta Neja.
Ya kara da cewa cimma wannan matsaya ta samo asali ne duba da yadda aiki yayi yawa ga ma’aikatar sufurin, wadda yanzu haka zata samu damar duba kan wasu ayyukan da suka shafi sufurin.
Babban sakataren ya kuma umarci hukumar NITMA ta tsawaita aikinta zuwa awanni 24, domin ci gaba da binciken ababan hawa da kula da motsin su baki daya.
A wani labarin kuma: Hukumar EFCC Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Sakin Tsohon Gwamna
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da mai shari’a C.L Dabup na babbar kotun jihar Filato ya yanke tare da wanke tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, da tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar Yusuf Pam.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya shaida wa Daily trust cewa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara shirin daukaka kara a kan zargin damfara da ake yi wa jami’an gwamnatin biyu.