By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana alhininsa kan gobarar data tashi a cibiyar kiwon lafiya matakin farko ta hanyar Gwari a unguwar Nasarawa A cikin karamar hukumar Chanchaga a jihar.
Da yake duba wurin, gwamnan yace za a sake gina shi nan take idan aka yi la’akari da yawan mutanen dake cin gajiyar ginin, duk da irin barnar da gobarar ta yi da yawa sosai.
A halin da ake ciki, yace, za a samar da wata hanya dabam ga marasa lafiya, don bada damar ci gaba da samar da ayyukan jinya ga jama’a har sai an kammala aikin sake gina asibitin.”Ina iya ganin babu wani abu da ya rage na ginin. Idan za mu yi aiki mai kyau, za mu sake gina shi gaba ɗaya.
“Dole ne a sake gina ginin gaba daya saboda muna da wasu majinyata a nan kuma dole ne mu nemo madadin wurin da za mu iya motsa wadannan majinyata, amma girman barnar na bukatar gyara da kayan aiki,” in ji shi.
Gwamna Bello ya lura cewa matakin lalacewa yana da yawa. Sai dai ya godewa Allah da ba a rasa rai ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnan yace “Abin takaici, mun yi asarar yawancin kayan aikin. Magunguna sun tafi, kantin magani sun tafi, bayanan sun tafi kuma kusan komai ya tafi, amma alhamdulillahi ba a samu asarar rai ba,” inji shi.sannan ya yabawa kokarin da hukumar kashe gobara tayi kan lamarin.
Kazalika Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ingantattun ma’aikatun PHC a kowace shiyya a jihar, inda yace sun samar da kayan aiki, da inganta su, da kuma samar da ma’aikata kusan dukkanin PHCs.