Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar da babu aiki a jihar yayin da wa’adin rajistar masu kada kuri’a a babban zaben 2023 yake zuwa karshe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta ranar Lahadin data gabata ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Kunle Somorin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/karfin-mummunar-dabiar-sayen-kuria-yana-barazana-ga-dimokuradiyyar-najeriya-sanusi/
Abiodun ya ce, “Bikin hutun kwana daya shi ne a samar da wata kafa ga dukkan ma’aikatan jihar da zasu samu dama, wadanda ko dai sun rasa katinsu na zabe, ko ba su yi rajista ba, ko kuma wadanda za su iya zuwa unguwanninsu, kananan hukumomi da mazabunsu don kammala yin Rijistar masu kada kuri’a ko canja katinsu, a inda ya dace, domin ba su damar shiga zabe mai zuwa”.
“A matsayin gwamnati mai haɗa kai, mai shiga tsakani, aikin PVC ga ‘yan ƙasa ba za a iya ƙarasa shi ba”.
Don haka Gwamnan ya bukaci dukkan manyan da suka cancanta da su yi amfani da damar hutun su koma gida zuwa unguwanni da mazabunsu daban-daban domin neman katin zabe da aka yi musu rajista.
Sannan yace yana da kyau su cike fom na korafi da rashin amincewa da kuma mika katin zabe na PVC a inda ya dace.
A Wani Labarin Kuma wani mutum dan shekara 62 a jihar Adamawa ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade da aka bashi amanarta.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa mutumin mai suna Godwin Sanda, mai sana’ar sayar da maganin gargajiya, ya yi amfani da yarinyar, mai tabin hankali da aka kawo masa domin ya yi magani, a cewar ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a ranar Lahadin, inda ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargin a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, bisa laifin aikata laifin fyade.
“Wanda ake zargin, Godwin Sanda, mazaunin kauyen Zagun, cikin karamar hukumar Numan, ya yi amfani da matsayinsa na mai bada maganin gargajiya don yowa yarinyar fyade da sunan neman magani,” in ji sanarwar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda Suleiman Nguroje, ta ce mahaifiyar yarinyar, Maryam Abubakar ta kai rahoton faruwar lamarin ga hedikwatar ‘yan sanda da ke Numan.
“Bincike na farko ya nuna cewa wacce aka lamarin ya shafa tana fama da tabin hankali kuma mahaifiyarta ta garzaya da yarinyar ne wajan wanda zargin domin neman magani.
“A cikin wani yanayi na daban, wanda ake zargin ya shawarci mahaifiyar da ta koma gida har zuwa lokacin da wanda aka kawo zata warke, kuma sakamakon rashin mahaifiyar na tsawon kwanaki biyar ne wanda ake zargin ya samu yin lalata da yarinyar ba bisa ka’ida ba.,” ‘yan sandan sun bayyana.
Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda na CID na gudanar da bincike kan wanda ake zargin bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Sikiru. Akande