Gwamnatin Jihar Ogun tayi barazanar korar wasu dalibai daga makarantun su, bayan da aka samu wasu bata gari da suka zane malaman sikandire akai akai a wasu yankunan jihar.
Ko da a ranar Litinin, sai da wasu bata gari suka suka yiwa wata makarantar sikandire kawanya, tare da tozarta malaman a idon dalibansu ta hanyar korar su, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban makarantar ne suka hayo bata garin.
Kawo yanzu dai malamai biyu aka samu rahoton sun raunata, sakamakon abinda bata garin suka aikata musu.
Da yake mayar da martani kan wadannan tagwayen hare haren da aka kaiwa malaman, kwamishinan ilimi, kimiyya da Fasaha na jihar Farfesa Abayomi ya ce duk dalibin da suka samu da laifi makamancin hakan zasu gurfanar da shi gaban ƙuliya, bayan sun kore shi daga karatu.