By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an gwamnatin jihar Ogun a ranar Alhamis sun rufe babbar kasuwar Kuto da ke Abeokuta, babban birnin jihar saboda rashin tsafta a cikin kasuwar da kewaye.
Jami’an sun kuma rufe wani fitaccen babban kanti da kuma kasuwar Oba Lipede saboda karya dokokin muhalli a jihar.
Wakilinmu ya lura da cewa tulin shara da zubar da sharar ba gaira ba dalili sun mamaye duk fadin kasuwar duk da kwandon zuba shara na jama’a.
Mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin muhalli, Ola Oresanya ya ce an rufe kasuwannin ne domin dawo da hayyacin kasuwannin.
Ya ce, “Wannan matakin ya zama wajibi domin kaucewa bala’i da tabbatar da lafiyar al’umma duk da gargadin da aka yi a baya da kuma ganawa da shugabannin kasuwar.”