By Abbas Yakubu Yaura
An dakatar da wani malamin makarantar Masifa Community Grammar, dake Masifa-Ile, jihar Osun, mai suna Philip Akinyemi, bisa zarginsa da shiga harkokin siyasa.
An kuma zarge shi da yin amfani da kalaman rashin gaskiya ga gwamnan jihar,Adegboyega Oyetola.
Wasikar dakatar da malamin, wacce wakilinmu ya gani a ranar Laraba, wanda ofishin kula da ilimi na Osun- ta yamma ya fitar mai dauke da kwanan wata 20 ga Disamba, 2021.
Kafin dakatar da shi, tun da farko ofishin Tutor-Janar ya nemi ganin Akinyemi dan gargadin sa.
Takardar da katarwar ta kara da cewa, “Akwai rubuce-rubucen da kuke yi a kafafen sada zumunta na zamani suna tada hankali da kuma nuna cewa kun kauce daga abin da aka dauke ku aiki a matsayin malami. Ka fi mayar da hankali kan siyasar bangaranci fiye da aikinka na malami da jajircewarka ga gwamnatin jiha a matsayinka na ma’aikacin gwamnati a jihar Osun.
Kalamanku da rubuce-rubucenku sun nuna rashin mutunta gwamnatin jihar da ke da himma wajen biyan albashin ku akai-akai. Bincike ya nuna cewa mutane da yawa sun gargade ku game da irin wannan rubuce-rubuce na tsokana da cece-kuce, ciki har da abokan aikinku da Shugaban makarantar, amma kun yi kunnen uwar shegu da gargaɗin da ake yi muku”
Bayan gudanar da bincike kan lamarin, wasikar dakatar da malamin, wanda kuma wakilinmu ya samu, ta ce matakin da Akinyemi ya dauka ya hada da cin zarafin jama’a da yayi ga hukumar da abin ya shafa.
Da aka tuntubi mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin ilimi Jamiu Olawumi, ya bayyana cewa abokanan aikin Akinyemi sun shigar da kara akan sa kan sa hannun sa a jam’iyyar wanda suka ce yana shafar aikin sa na farko.