By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Filato ta yi gargadin cewa za ta rufe duk wasu gidajen mai da ke tara man fetur a jihar.
Gwamnatin jihar ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Danladi Atu, ya fitar a Jos.
Gwamnati ta lura da matukar damuwa, kan yadda wasu gidajen mai ke boye man fetur, da nufin haifar da karanci sa na wucin gadi, wanda hakan yake haifar da wahalhalu ga matafiya da sauran masu amfani da kayyakin mai.
A cewar SSG, kwamitin gudanarwa na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa da kuma masu duba ababen hawa an ba su umarni da su tabbatar da cewa an yi hakan.
Atu ya ce, “An kuma umarci rundunar da ta rufe duk wani gidan mai da aka samu yana yin gwanjon kayayyakin.”