By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Ribas ta sanar da sauke wasu shugabanni 14 na makarantun gwamnati, tare da janye lasisin gudanar da ayyukan wasu makarantu masu zaman kansu 21 bisa zarginsu da hannu a tabka magudin jarabawa.
DUBA WANNAN LABARIN: An Tsinci Gawar Wata Mata A Cikin Otal A Jihar Benue
Kwamishinan Ilimi na jihar Farfesa Kaniye Ebeku ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fatakwal ranar Litinin.
Ebeku ya ce matakin ya biyo bayan wata wasika da hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma ta rubutawa ma’aikatar ilimi ta jihar mai dauke da jerin sunayen makarantun sakandire 35 a jihar da aka yi watsi da su sakamakon rashin gudanar da jarabawar WAEC a shekarar 2021.
Kwamishinan ya ce, “Mun samu takarda daga WAEC mai dauke da jerin sunayen makarantun sakandare 35 a jihar da aka cire saboda rubuta jarabawar WAEC da kuma laifukan da suka aikata.
“Hakan ya dame ni kan yadda aka gano cewa an tabka kura-kurai wajen gudanar da jarabawar bara.
“Bayan samun takardar, nan take muka gayyaci makarantun da abin ya shafa zuwa taro ganawa dasu.
“Mun gabatar musu da wadannan bayanai, kuma muka gano cewa wadanda ke kan madafun iko a makarantu daban-daban sun bari irin wannan lamari ya faru. Bayan haka, mun yanke shawarar daukar wasu takunkumi akan su.
“Ga dukkan shugabannin makarantun da ke kan hidima kuma wadanda suka yi aiki a lokacin da lamarin ya taso, mun ba da umarnin a rage musu mukamai.
“Ga dukkan makarantun da aka samu a cikin jerin, mun ba da umarnin a cire lasisin gudanar da aikinsu nan take.”
Ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike ba ta amince da duk wani nau’i na tabarbarewar jarabawa ba, walau a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Comments 2