Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal a ranar Talata ya raba kayan tallafi na kayayyakin daban-daban ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a karamar hukumar Silame a jihar. Gwamnan ya tallafawa akalla iyalai 9, 000 wadanda ambaliyar ruwan ya shafa.
Da yake ba da tallafin ga wadanda abin ya shafa a Katami, wani kauye a karkashin Silame, Tambuwal ya ce sun kashe akalla naira miliyan 40 wajen siyan kayayyakin da aka raba wadanda suka hada da masara, gero, da kuma dawa tare da kayayyakin sanyawa.
Gwamnan ya tabbatar da cewa; duba da irin yadda ambaliyar ruwan ya shafi mutane da dama, za su tabbata sun kara tallafawa wadanda abin ya shafa da wadansu kayayyakin.
A karshe ya nuna alhininsa bisa wannan ibtila’in da ya shafe su, sannan ya yi musu addu’ar Allah ya kiyaye aukuwar hakan a gaba a duk fadin jihar da ma kasa baki daya.