Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom a ranar Litinin ya ƙalubalanci Gwamnatin shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ortom yace gwamnati da tafi kowacce lalacewa ta Sojoji a Ƙasar, tafi Gwamnati mai ci a yanzu ta APC.
Ortom ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambaya daga ƴan jarida a Makurɗi, Babban Birnin Jahar Benue, jim kaɗan bayan ya dawo daga Zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar PDP a Abuja.

KARANTA WANNAN LABARIN:Ku ayyana ƴan bindiga a matsayin ma’aikatan Gwamnati — Shehu Sani ya buƙaci Gwmanatin Tarayya
Yace sakamakon abinda ya fito daga taron zaɓen shuwagabannin, wata alama ce Jam’iyyar PDP ta sanya kanta a wata turba ta karɓe Shuwagabancin Ƙasar a shekarar 2023, yana mai zargin cewa Gwamnatin APC ta faɗi ƙasa warwas.
“Mu PDP muna ƙudirin karɓar ragamar shugabancin ƙasar a shekarar 2023, sabudda gwamnatin APC ta kasa.
“Sun kasa samar da tsaro,sun lalata tattalin arziki, kuma na karanta tarihin wanda suka lalata Najeriya akwai Sojoji, amma gwamnatin soji da tafi kowacce lalacewa tafi ta yanzu.
Gwamnan ya kuma yabawa ƴan uwansa Gwamnoni da suka yi ƙoƙari wajen ganin an cimma nasara na zaɓen shuwagabannin da kashi 90.
Comments 1