Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ya kare matakinsa na jibje cin-ci-rundun dakarun sojin kasar a kusa da gidan Mataimakin Shugaban Kasar na farko Riek Machar
Salva Kirr ya Kuma bayyana cewa wannan mataki ne wanda aka saba da shi, domin kare jagoran yan awaren.
Anashi bangaren Mr Machar yayi Allah wadai da wannan mataki inda ya ce, hakan zai haifar da rashin tabbas, Kuma zai iya shafar Kudirin da ake son cimma wa na samar da zaman lafiya a kasar.
A dai makwannin baya-bayan nan ne Machar ya zargi dakarun sojin gwamnatin Sudan ta Kudu da kai wasu hare -hare a jihohin Upper Nile da kuma Unity dake Arewacin kasar.
A halin da ake ciki dai, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin biyu da su tattauna don dakile kasar Sudan ta Kudu komawa cikin yakin basasa.