Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta sake zama teburin tattaunawa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya.
Taron ranar Talata shine karo na biyu da akayi, tun bayan da Ƙungiyar ta ayyana yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya.
Malaman suna so a kara masu walwalar su, da farfaɗo da Jami’o’in Najeriya, da kuma basu gashin kansu da sauran buƙatu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta kori Shuwagabannin APC a Taraba
Wakilan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya da suka halarci taron, sunce basu wani ra’ayin sake sa hannu akan wata yarjejeniya fahimta.
Suna buƙatar ayi aiki akan yarjejeniyar da akayi a baya.
Haka zalika, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bayyana fatan cewa zasu shawo kan lamarin.
Dukkanin ɓangarorin guda biyu sun ki amincewa akan wanda ke kawo tsaiko akan tabbatar da tsarin biyan Albashi na suka ɓullo dashi na UTAS.
A yayinda Ministan ya bayyana cewa Ƙungiyar na kawo tsaiko akan amfani da tsarin UTAS da Hukumar NITDA, Malaman sun jajirce akan cewa NITDA bata shirya karɓar su ba.
Rashin amincewa akan tsarin biyan Albashi yana ɗaya daga cikin Malaman suka lissafo wanda ya sanya suka shiga yajin aiki.