Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a biyu da kuma Litinin biyar ga watan Afirelun wannan shekara a matsayin ranr hutu don bukuwar Easter.
Wannan sanarwa ta zo ne ta bakin Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola cikin wata sanarwa mai dauke da dangwala hannun Jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Muhammad Manga a yau Talata.
Sanarwa ta ja hankalin al’ummar kiristci da su rungumi dabiun yafiya da jin kai da kauna da hakuri gami da zaman lafiya kamar yadda Isah Almasihub ya yi.
Kazalika Aregbesola ya jaddda bukatar dake akwai ga krisitocibn da su yi mafani da wannan lokcai na bukukuwa wajen yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban kasar nan.
Har wa yau Ministan ya tabo matsalar tsaro dake addabar kasar nan inda ya ce gwamanti ba za ta ragar ma kowa ba musamman masu garkuwa da mutane da matsalar fashin daji da dukkannin nauin miyagun ayyuka da suka yi wa kasar nan daurin huhun goron.
Da yake taya alummar Kiristoci murnar zagayowar wannan ranar, Rauf Aregbesola ya kuma bukaci yan kasa da su tashi tsaye su bada gudunmawar su wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari don gina kasar nan da ma yan kasar.