Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya ce Kasar nan tana cikin halin tausayi na rashi kuɗi.
Da yake magana a a yayin wani Shiri a Jihar, Gwamna Obaseki ya ce wannan rashin kuɗi ya sa ala tilas tallafin da jihohi ke samu ya kasa, lamarin da ya kai ga sai gwamnatin tarayya ta buga kudi sabo fil har naira biliyan hamsin zuwa sittin din baiwa Jihohin su kasafta a watan Maris.
Ya ce “Lokacin da Muka je taron kwamitin asusun tallafin kudi na gwamnatin tarayya, gwamantin tarayya ta sa an buga kudi har naira biliyan hamsin zuwa sittin don yin guzuri a kan wanda ake da shi”
Da yake tsokaci kan yawan dogaro da man fetur da kasar nan ie yi, ya ce yawan basussuka dake yi mata katutu abin dubawa ne
Tun bayan yakin basasa muke ta maganganu cewa Najeriya bata da Matsalar kudi indai za mu ci gaba da fitar da mai.