Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta NLC ta ce kiraye-kiraye da ta yi samu daga gwamnatin tarayya ne ya sa ta janye yajin aikin gargadi na kwana biyar da ta tsunduma.
Kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne don tursasawa gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i janye kora dubban ma’aikata a Jihar.
To sai dai bisa ga dukkan alamu yajin aikin ya jefa al’ummar gari ciki halin ƙaƙanikayi, domin kusan ko wane ɓangaren aiki ya tsaya chak sakamakon rufe su da ma’aikata suka yi.
Tun sa farko ne gwamna el-Rufa’i ya bayyana matsayarsa kan yajin aiki , inda ya ce babu gudu babu ja da baya dangane da matakin da ya dauka na korar ma’aikatan.
Ga alamu kuma alwashin nashi ya zamo gaskiya domin a daren yau ne shugaban NLC Kwamared Ayuba Wabba ya sanar da janye yajin aikin baya wani taron gaggawa da suka gudanar inda ya ce gwamnatin tarayya ce ta tsoma bakin ta cikin lamarin har ya kawo karshe.