Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ya hana mambobin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) damar shiga dandalinsa.
Da yake magana a Abuja jiya a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce “haramtattun kungiyoyin ta’addanci” suna amfani da dandalin wajen ayyukan tada kayar baya da kuma tada zaune tsaye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Filato Ta Rufe Dukkan Makarantu Masu Zaman Kansu, Ta Soke Lasisin Su
Ya ce: “Muna son Kamfanin Google ya duba yadda za a magance amfani da tashoshi masu zaman kansu da na YouTube da ba a jera su ba da kuma gidajen rediyon YouTube na haramtattun kungiyoyin ta’addanci.”
“Tashoshi da imel da ke dauke da sunayen kungiyoyin da aka haramta da kuma masu alaka da su bai kamata a bar su a dandalin Google ba,”in ji shi.
Mohammed ya ce ‘yan Najeriya na cikin wadanda suka fi yin amfani da kafafen sada zumunta a duniya, inda sama da miliyan 100 ke amfani da intanet.
Ya ce, duk da haka, wadanda ba su da mutunci ko kungiyoyi suma suna amfani da wadannan kafafan domin yin zagon kasa da aikata munanan ayyuka.
Ministan ya lura cewa a kwanan baya gwamnati ta ba da shawarar wani ka’idar aiki don hulɗar sabis na na’ura mai kwakwalwa / Intanet “don samar da tsarin haɗin gwiwar kare masu amfani da safukan intanet na Najeriya.
Darektan Google na yankin kudu da hamadar sahara, al’amuran gwamnati da manufofin jama’a, Charles Murito, ya ce dandalin ya bullo da wani shiri mai suna “Trusted Flaggers” ga ‘yan kasar da aka horar da su wajen bibiyar abubuwan da ke cikin intanet domin nuna abubuwan da ke da matukar damuwa.
Manajan Harkokin Gwamnati da Harkokin Jama’a na Google, Adewolu Adene, ya ce ta hanyar Google News Initiative Challenge, kafofin watsa labarai 30, biyar daga Najeriya, ciki har da dandali na duba gaskiya, za a ba su kyautar dala miliyan $3.2 don karrama ayyukan da suka kirkira a ciki watsa bayanai.
Ya ce Google zai yi aiki tare da ma’aikatar yada labarai da al’adu don ƙididdige kayan tarihi da aka dawo da su kwanan nan don adanawa tare da tallata su ga masu sauraro na duniya ta hanyar fasahar Google da Al’adu.