By Abbas Yakubu Yaura
Makonni shida bayan da likitoci masu neman kwarewar aiki karkashin kungiyar likitocin ta Najeriya suka yi watsi da ayyukan da suke yi na masana’antu a fadin kasar, har yanzu gwamnatin tarayya ba ta cimma wasu yarjejeniyoyin data rattabawa kungiyar ba a cikin yarjejeniyar fahimtar juna.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar 4 ga watan Oktoba, NARD ta janye yajin aikin na watanni biyu data keyi.
Daga cikin korafe-korafen Hukumar NARD akwai jinkirin da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen raba kudaden horar da Ma’aikatan Lafiya ga Likitoci masu neman kwarewar aiki.
Kungiyar ta kuma yi tir da irin wahalhalun da mambobinta ke fuskanta a tsarin hada-hadar kudi na gwamnati da suke fuskanta sakamakon tsaikon biyan albashin su daga watanni uku zuwa bakwai.
A lokacin yajin aikin, Gwamnatin Tarayya ta hannun Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ta bayar da umarni na rashin biyan albashi ga manyan Daraktocin Asibitoci tare da cewa ba za a rika biyan likitocin dake neman kwarewar aiki ba a cikin watannin da suka yi aiki da kuma wadanda basu yi aiki ba.
Ministan wanda yake tare da Ministan Kwadago, Chris Ngige, sun kuma kai karar likitocin zuwa kotun masana’antu.sai dai kuma bayan tattaunawa, NARD ta sami biyan wasu buƙatu. Wannan ya kai ga janye yajin aikin.
Da yake zantawa da jaridar PUNCH a Abuja, Shugaban NARD na kasa, Godiya Ishaya, yace gwamnati ba ta janye karar ba, ballantana ta biya basussukan da kungiyar take binta.
Sannan yace, “har yanzu shari’ar tana gaban kotu; a cikin takardar fahimtarmu ne za su janye shi da zarar mun janye yajin aikin. Yanzu haka mun koma fiye da makonni shida amma har yanzu shari’ar tana nan a kotu.Ko albashin ma ba a biya ba”.
A Kokarin jin ta bakin Ngige da Ehanire ya ci tura domin basu amsa kiran da aka yi ta yi musu ba.har lokacin kammala wannan rahoton.