Kwamitin kula da rabon kudin asusun gwamnatin tarayya ga jihohi, da kananan hukumomi, (FAAC) ya raba kudi kimanin Naira Biliyan 760.717 ga Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi. A matsayin kudin da aka samu a kasar ta bangaren shiga a watan July na 2021.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata takardar bayan taro da Kwamitin ya fitar, bayan kammala taron daya saba gudanarwa kowanne wata domin duba kam wata gaba, kuma taron an gudanar da shi ne ta kafar Internet.
Jimillar kudin da aka rarraba yakai naira biliyan 760.717, Kudaden shiga musamman daga jihohi da sauran bangaren bayar da kudin shiga yakai naira biliyan 617.705. yayin da kuwa bangaren kudin haraji musamman kan kayayyaki da sauransu, (VAT) aka samu kudi naira Biliyan 140.555. sai kuma ɓangaren musayar kudade wanda aka samu ribar naira biliyan 2.457.
Takardar bayan taron ta kuma tabbatar da jimilar adadin kudaden da aka rarraba na naira biliyan 760.717 wanda gwamnatin tarayya ta karbi naira Biliyan 321.226, Jihohi kuwa sun karbi naira Biliyan 222.514, sai kuma kananan hukumomin inda suka karbi naira biliyan 166.562.
Jimillar kudaden da aka rarrabawa jihohi yakai naira Biliyan 50.415, wato dai kaso sha uku na Kudaden shiga da aka rarraba.