By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin Tarayya tace za ta iya dakatar da biyan albashin ma’aikatanta guda 1,173 a watan Janairu saboda gazawarta wajen inganta bayanan su na tsarin hada-hadar ma’aikata da kuma tsarin biyan albashi.
Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata da’ira mai lamba HCSF/PS/CMO/POL.III/T/62, wadda wakilinmu a Abuja ya samu.
Sanarwar wacce ta fito daga ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya mai suna
“Gudanar da bayanan albarkatun IPPIS don duba bayanan ga ma’aikatan dake aiki a kasashen waje na Najeriya.
Babban Sakatare, Ofishin Gudanar da Ma’aikata, Dokta Marcus Ogunbiyi shine wanda ya sanya hannu, kuma an gabatar da shi ga ma’aikatan da abin ya shafa da kuma jerin ‘A’ dake kunshe a cikin daftarin.
Sanarwar ta kuma tabbatar da adadin ma’aikata guda 1,173.
Sannan Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya amince da bude kofar tantance bayanan IPPIS ga jami’an da ba su sabunta bayanansu ba kamar yadda aka umarce su a baya. Ranar rufewa ita ce Juma’a 7 ga watan Janairu sabuwar shekara ta 2022.
“Saboda abubuwan da ke sama, an shawarci duk jami’an da abin ya shafa kamar yadda ke kunshe a cikin jerin sunayen da aka makala da su ziyarci tashar tabbatar da IPPIS don sabunta bayanan su ba da jimawa ba da aka bayyana ranar rufewa.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa ana ci gaba da cece-kuce a kan shigar da tsarin IPPIS a matsayin tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Fitattun kungiyoyi irinsu Kungiyar Malaman Jami’o’i, da Manyan Ma’aikatan Jami’o’i da Kungiyar Likitoci ta Kasa, da dai sauransu, sun ci gaba da kokawa kan rashin daidaito a cikin tsarin na IPPIS.
Gwamnatin Tarayya ta dage cewa ba za ta biya ma’aikatan da suka kasa yin rajista a dandalin ba.
Yayin da aka kebe ‘yan kungiyar ASUU a wani bangare, an kuma umarci sauran ma’aikatan gwamnati musamman ma’aikatan gwamnatin tarayya da su yi rajista a dandalin.