Gwamnatin tarayya ta gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2023, da aka kiyasta zai kai Naira Tiriliyan 19.76, yayin da gibin zai tashi tsakanin N11.30tn zuwa N12.41tn a kasafin shekarar 2023.
Idan gibin ya daidaita a kan N12.41tn a shekarar 2023, gwamnatin tarayya na iya bukatar rancen kudi don cike shi, wanda zai iya kara yawan bashin da ake bin Najeriya zuwa Naira Tiriliyan 54.01.
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito cewa Bashin ake bin Najeriya a halin yanzu ya kai Naira Tiriliyan 41.6, bisa ga bayanan watanni hudu na farko na shekarar 2022 daga ofishin kula da basussuka.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Kano Na Shirin Rushe Wasu Gine-Gine Da Dama A Jihar
Mai yiyuwa ne bashin zai wuce kaso uku cikin 100 da aka kayyade a cikin kan jumullar Kudin, wanda a baya gwamnatin da ke ci a yanzu ta wuce gona da iri a shekarar 2020.
Ministar kudi kasafi da tsare tsaren kasa Zainab Shamsuna Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da ta hallara gaban kwamitin kudi na majalisar wakilan kasar domin gabatar da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi na shekarar 2023 zuwa 2025.
Yayin da take bayanin hanyoyin biyu da za a cike gibin ga kwamitin, Ministar ta ce hanya ta farko ta hadar da ci gaba da biyan tallafin man fetur a ilahirin shekarar 2023
Ta ce hanya ta farko an yi hasashen cewa gibin zai kai naira Tiriliyan 12.41 a 2023, idan haka bi wannan hanya gwamnati za ta kashe tiriliyan shida kan tallafin man fetur
Hanya ta biyu kuma ta kunshi ci gaba da biyan tallafi zuwa watan Yunin 2023, a wannan kuma gibin zai kai naira Tiriliyan 11.30, inda ake hasashen tallafin da za a biya zai kai naira tiriyan 3.3
A wani labarin kuma: Atiku Ya Bada Tallafin Naira Miliyan 50 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kano
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasuwar Kantin-Kwari da ke Kano. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayar da gudunmawar ne a ranar Litinin, a Kano, a wani taron karbar tsohon gwamnan jihar Kano, Sen. Ibrahim Shakarau, a cikin jam’iyyar daga New Nigeria Peoples Party (NNPP).