Gwamnatin tarayya sunyi Bikin Satin Ma’aikata
A cikin yunkuri da gwamantin tarayya keyi ta samar da bikin satin Ma’aikata domin bada kyauta ga ma’aikata wadanda sukai aiki tukuru a lokacin cutar Covid-19.
Bikin dai wanda mahukunta dake tarayya sukayi don yanama jajirtattun ma’aikata da sukai aiki ba dare ba rana har lokacin annobar covi-19.
KARANTA:- Mutanen Garin Lafiya na Tafiyar kilomita 200 don Zuwa Babban Asibiti
Sakataren gwamnatin tarayya na dindindin Tijjani Umar yake bada kyauta ga Waheed Shabonde dake aiki a jaha ta fannin kafafen yada labarai kan irin kokarin da yayi akan aikinsa a Abuja.
Umar Tijjani Yana Mika kyauta ga Dr. Ebuta Agbor dake aiki a Asibitin jaha kan irin jajirtaccen aikin da yayi duk da barkewar cutar Covid-19 ranar 25 ga watan Yuni 2021.
Sakataren Jaha Tijjani Umar yana bada kyauta ga Hosea Yahsim babban matukin mota dake aiki a Jahar kan irin kokarin da yayi akan aikinsa.