Gwamnatin tarayya ta bayar da tireloli 116 na hatsi domin tallafa wa mabuƙata da masu karamin ƙarfi a jihar Bauchi a matsayin tallafin Korona.
Ma’aikatar Agaji da kyautata rayuwa ta sanar da miƙa tallafin da aka fitar daga rumbun gwamnatin tarayya bayan amincewa da rabon kayan abincin a jihar Bauchi.
Ministar ma’aikatar Sadiya Umar Farouk ta ce hatsin da aka bayar sun haɗa da masara da dawa da kuma gero.
Da yake karɓar kayan, mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yaƙi da cutar Korona na jihar ya yi alƙawarin raba kayan ga waɗanda suka cancnata.
Ya kuma yaba da samun tallafin wanda zai taimaka waje rage tasirin da ɓullar cutar ta haifar wa jama’a.