Gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biyan karin albashin kashi 23.5 na dukkan malaman jami’o’in dake fadin tarayya, in ban da shehunan malaman jami’o’i, wanda za a sake dubasu tare da kara musu kashi 35 cikin 100.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi tawagar gwamnatin da ke cikin tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aiki kan sanya hannu kan duk wata yarjejeniya da gwamnati ba za ta iya aiwatar da ita ba.
Shugaban ya kuma umurci tawagar gwamnati da ta shawo kan malaman jami’o’in su koma bakin aiki.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan jiya Talata, a Abuja yayin wata ganawa da shugabannin jami’o’in tarayya da masu goyon bayan shugabannin jami’o’in fadin kasar kan shawarar da gwamnati ta cimma na kawo karshen yajin aikin da ASUU ke yi.
KARANTA ANAN: 2023: Ba Za A Hana ‘Yan Gudun Hijira Hakkinsu Na Kada Kuri’a Ba — INEC
Adamu ya ce bayan ganawa da Buhari da ministocin kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa; sadarwa da tattalin arzikin na zamani; da ilimi da kuma babban daraktan ofishin kasafin kudi da shugaban hukumar bayar da albashi.
To sai dai sun ce daftarin yarjejeniyar da kwamitin Nimi Briggs ya yi nazari sosai kan batun karin albashin da aka yi la’akari da shi ba domin ya sabawa halin da ake ciki yanzu, idan aka yi duba da tattalin arzikin kasar.
Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta dakatar da ayyukan ta na tsawon kwanaki sama da 200 yanzu haka, saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan dukkan bukatunta, wadanda suka hada da kammala shirin sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU ta shekarar 2009, da sauransu.
A wani labarin kuma: Liz Truss ta nada Kemi Badenoch, wasu a matsayin mambobin majalisar ministocinta
Firaministar Burtaniya, Liz Truss, ta nada Kemi Badenoch a matsayin mamba a tawagarta a wani sauyi a majalisar ministocinta bayan da Truss ta karbi mukamin a ranar Talata.
Wani sakon da aka wallafa a shafinta na Twitter mai inganci, na Firaministar Burtaniya, @10DowningStreet, a ranar Talata, ya bayyana cewa an nada Badenoch a matsayin Sakatariyar Harkokin Kasuwancin Kasa da Kasa kuma Shugabar Hukumar Kasuwanci.