Ministan Kwadago da ayyuka na tarayya Festus Keyamo ya ce Majalisar Zartaswar tarayya ta amince da shirin ɗaukar ma’aikata na musamman da gwamnatin tarayya ke yi ya kasance shekara-shekara.
Keyamo ya bayyana haka ne a birnin tarayya Abuja yayin zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa.
Idan ba a manta ba, a watan Janairu ne gwamnatin ta fitar da tsarin daukar ma’aikatan inda za a rika biyan kowane mai sana’ar hannu naira dubu ashirin har na tsawon wata uku din dogaro da kai.
Ya ce “ba za mu bar shirin nan ya tafi a banza ba, don haka majalisar zartaswa ta kasa ta amince da shi, abinda muke jira kawai yanzu shine kudaden biyan da za mu fara aiwatar da shi”
“Kowa ya san wannan ne karon farko da ake irin wannan tsari a Najeriya, akwai tsare-tsare da muke yi, hakan ne ma ya da muka samu jinkiri, amma komai zai yi saiti nan gaba kaɗan”
Ministan ya ce kawo yanzu an biya kudi sama da N24,000, 871,000.00 ga mutane kimanin dubu ɗari hudu da sha uku da dari shida da talati a farkon tsarin bada tallafin.
Ko da yake jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dubban mutane na nan sun yi zaman dirshan suna jiran kudin su da ba a biya ba.
Sai dai Keyamo ya ce jinkirin da aka samu ya biyo bayan kalubale ne da aka yi ta fuskanta musamman wurin bada lambar shaidar banki ta BVN.