By Ishaq Dabai
Jihar Filato ta karbi kayan agaji na kimanin Naira miliyan 100 daga Gwamnatin Tarayya don rabawa ga wadanda harin ‘yan bindiga ya ritsa da su a jihar.
Ministar kula da ayyukan jin kai da kula da bala’oi da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta gabatar da kayayyakin agajin ga gwamna Simon Lalong a wani dan takaitaccen biki da aka yi a barikin runduna ta 3 dake karamar hukumar Bassa a ranar Talata.
Ministan tace kayan sun cika alkawuran da suka yi wa Gwamnan lokacin daya ziyarci Shugaban kasa ya nemi taimako ga wadanda abin ya shafa.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamna, Macham Makut, ya ambato ministan tana cewa,“Abubuwan da suka kai kusan Naira miliyan 100 sun kunshi abinci da kayan da ba na abinci ba kamar zanen rufi, kusoshi, siminti, shinkafa, masara, sabulu da katifu da sauransu, kuma ana nufin taimakawa mutane su dan su dawo su zauna da kafafunsu. ”
Lalong yace duk da an yaba da wannan karamci, amma yanayin dake haifar da lamarin ya sanya bikin ya zama na musamman saboda asarar rayuka da dukiyoyi da akayi. ”