Ma’aikatar agajin gaggawa da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya ta raba jimillar Naira miliyan 1 ga tsofaffi 50 a Jihar Benue a matsayin jarin farko don ci gaban tattalin arzikinsu.
Ministar agajin, Sadiya Umar Farouq, wacce ta bayyana hakan a lokacin wani horo na kwanaki biyu, ta ce kwarewar da aka samu a shirin zai taimaka matuka wajen magance musu kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ke fuskantar su.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/2023-inec-ta-musanta-amincewa-da-lawan-akpabio-a-matsayin-su-na-yan-takarar-sanata/
Ta ce, “Na gamsu cewa a karshen wannan shiri na koyon sana’o’i, gogewar da aka samu za ta taimaka matuka wajen magance kalubalen zamantakewa da tattalin arzikin da ke fuskantar su. Don haka na amince a ba wa mahalarta taron tallafin Naira 20,000 kowannensu a matsayin jarin mafari.”